Soke Aikin Hajji: Jihar Neja ta mayar da sama da naira biliyan ɗaya ga maniyyata

0
462

Hukumar Kula da Alhazai ta Jihar Neja ta bayyana cewa, ta maidawa maniyyatan jihar kuɗaɗensu sakamakon soke aikin Hajji ga ƴan ƙasar waje.

Sakataren hukumar, Alhaji Umar Makun Lapai, shi ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da kwamitin gudanarwa na hukumar.

Lapai ya bayyana cewa hukumar ta biya kuɗi har Naira biliyan ɗaya da miliyan ɗari biyu da ashirin da biyar da dubu ɗari biyar (1, 225, 500,000) ga maniyyata 834 daga sassan jihar.

Sai dai, sakataren ya bayyana rashin jin daɗin hukumar dangane da yadda wasu jami’an hukumar na shiyya suka nemi a maida wa maniyyata da kuɗaɗensu ba tare da sanin maniyyatan ba, wanda a ƙarshe tilas maniyyatan suka dangana da hukumar don neman mafita.

Alh Umar Makun ya nuna gamsuwarsa kan yadda kwamitin gudanarwar da ma ma’aikatan hukumar suke gudanar da ayyukansu yadda ya kamata duk da ƙalubalen annobara korona da ake fama da ita.

Sanarwar manema labarai da hukumar ta fitar ta hannun mai baiwa hukumar shawara kan sha’anin yaɗa labarai, Hassana Isah a ranar Laraba, ta nuna yadda Alh Makun ya yi fatan Allah Ya kawo ƙarshen wannan annoba da ta addabi duniya, tare da kira ga al’umma da a rungumi ƙaddara.

Yana mai cewa, bayan kowane tsanani sauƙi na nan tafe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here