An yi kira ga ma’aikatan hukumar Hajjin Legas da su ƙara zama jajirtattu

0
441

An yi kira ga ma’aikatan Hukumar Alhazai ta Jihar Legas da su zamo masu aiki tukuru game da ayyukansu.

Kwamishinan Harkokin Cikin Gida na Jihar Legas, Prince Anofiu Olanrewaju Elegushi shi ne ya wannan kira yayin taron bita na yini guda da aka shirya wa ma’aikatan hukumar ranar Alhamis a Legas.

Taron bitar mai taken: “Dabarun kasuwanci da sadarwa mai inganci ga aikin Hajji”, an shirya shi ne musamman don amfanin ma’aikatan hukumar, kuma irinsa kenan na farko tun bayan kafa hukumar a 1967.

An gudanar da bitar ne a babban zauren taro na Masallacin Shamsi Adisa Thomas (SAT) da ke GRA a yankin Ikeja.

Duba da irin muhimmancin da ayyukan hukumar ke da shi ya sanya Kwamishinan ya ja hankalin ma’aikatan da su gudanar da aikinsu bil haƙƙi ba tare da sa ran samun wani tukwici daga hannun maniyyata ba face a wajen Allah Maɗaukaki.

Daga nan ya yaba wa gwamnan jihar, Mr. Babajide Olusola Sanwo-Olu da mataimakinsa Dr. Kadri Obafemi Hamzat bisa irin goyon baya da kuma gudunmawar da suke ba wa hukumar alhazan jihar a harkokinta

Tare da ba su tabbacin cewa, a matsayinsu na jakadun Gwamnatin Jihar Legas a Kasar Sudiyya, hukumar za ta zage dantse wajen ɗaga darajar jihar ta hanyar ba da himma wajen yin abin da ya kamance ta na bai wa maniyyata cikakkiyar kulawar da ta dace.

Alhaji Bashir Ademuyiwa Braimah wanda tsohon ma’aikacin gwamnatin jihar ne, da kuma Mrs. Toyin Anjous-Ademuyiwa su ne suka gabatar da lacca a wajen taron.

Yayin da Alhaji Braimah ya nuna buƙatar da ke akwai na ma’aikatan su kasance masu wanzar da kyakkyawar mu’amala tsakaninsu da maniyyata, ita kuwa Anjous-Ademuyiwa cewa ta yi, ya kamata hukumar ta zamanto mai amfani da fasahar zamani wajen gudanar da harkokinta don cimma ƙudurorinta.

A nasa ɓagaren, Sakataren Hukumar, Mr. Rahman Ishola, yabo da godiya ya zazzaga wa Gwamnan jihar da ma mataimakinsa haɗa da Kwamishina Elegushi kan gudunmawar da suka bayar wajen ganin taron ya yi nasara.

Taron ya samu halarcin manya da ƙananan ma’aikatan hukumar da takwarorinsu, ciki har da: Mrs. Adetutu Ososanya; Mrs. Yetunde Badmus; Mrs. Yetunde Gbafe da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here