Ministan Harkokin Addinin Musulunci da Shawarwari na Saudi Arebiya, Abdullatif Al-Sheikh ya baiwa rassan ma’aikatar a lardinan masarautar da su dawo da majalisun haddar Ƙur’ani Mai Tsarki, wanda a kewa laƙabi da halaga a masallatai da kuma buɗe cibiyoyin koyon Ƙur’ani na mata.
Ministan ya kuma bada umarnin cewa sai waɗanda manhajar Tawakkalna ta nuna cewa yana da rigakafin kamuwa daga cuta bayan sun kammala ɗaukar alluran rigakafin korona cikakku ne za a bari su riƙa ɗaukar darussan.
Haka-zalika, dole ne a riƙa daukar dukkanin matakai na hana yaɗuwar korona a yayin zaman majalisun.
Za a tuna cewa, a ranar 9 ga watan Satumba, 2020 ne Minista Al-Sheikh ya bayar da umarnin rufe dukkanin ajujuwan darussan ilimin addini, muhadarori da kuma koyon karatun Alkur’ani a dukkanin masallatan Saudiya bayan ɓarkewar annobar korona.