Saudiya ta naɗa sabbin ministocin Hajj da Ummara da na lafiya

0
554

Saudi Arebiya ta naɗa tsohon Ministan Lafiya, Tawfiq Al-Rabiah a matsayin sabon Ministan Hajji da Ummara.

Haka-zalika an naɗa Fahd Al-Jalajel a matsayin sabon Ministan Lafiya.

A ranar Juma’a ne Masarautar Saudiyya ɗin ta rattaba hannu a wasu dokoki na masarauta da su ka haɗa da haɗin sabbin ministocin na lafiya da na Hajji da Ummara.

Haka kuma an cire Abdul Aziz bin Abdulrahman Al-Arifi a matsayin Mataimakin Ministan Harkokin Tafiye-tafiye, inda a ka naɗa shi a matsayin mai bada shawara a Babban Ofishin Majalisar Ministoci.

Haka shima Laftanal Janar Mutlaq bin Salem Al-Azima an ƙara masa girma zuwa matsayin Janar sannan a ka naɗa shi a matsayin shugaban rundunar tsaro ta haɗin gwiwa.

Sannan an kafa sabuwar Ma’aikatar Lura da ginin garuruwan Yanbu, Umluj, Al-Wajh da Duba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here