Babban Ofishin Kula da Harkokin Masallatan Harami Guda Biyu ya sanar da cire alamomin bada tazara da a ka sanya a Masallacin Harami na Makka sakamakon annobar korona.
Ofishin ya sanar da cire alamomin ne baya an idar da sallar Isha’i ta yau.
Sanarwar ta ce za a yi sallar asuba ta gobe da sawu kafaɗa da kafaɗa kamar yadda a ka saba kafin zuwan korona.