Saudiya ta soke kwanaki 14 da a ke yi kafin samun izinin Ummara

0
362

Ma’aikatar Hajji da Umurah ta Saudi Arebiya ta ce daga yanzu an soke tsarin jira na kwanaki 14 don neman samun izinin aiwatar da Ummara.

Shugaban tsare-tsare na ma’aikatar, Dr. Amr Al-Maddah, shi ne ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta Arab News.

Ya bayyana cewa tun bayan sassauta dokokin yaƙi da cutar korona, an samu ƙaruwar alhazan Ummara a Masallacin Harami.

Jami’in ya ce an ɗauki wannan mataki ne duba da yadda a ke samun ƙaruwar maniyyata, ganin haka ya sanya Ma’aikatar Hajji da Ummara ta soke tsarin zaman jira na kwanaki 14 don ci gaba da bai wa maniyyata dama.

A ranar 16 ga Oktoba ne Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ta bada sanarwar sassauta dokokin yaƙi da cutar korona a faɗin masarautar Saudiyya da ma dokokin da suka shafi Masallacin Makka, wanda hakan ya bada damar komai ya koma kamar yadda aka saba a baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here