Gwamnan Bauchi ya naɗa Abdulrahman Idris sabon shugaban hukumar alhazai ta jiha

0
87

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala AbdulKadir Muhammad, ya naɗa Dr AbdulRahaman I. Idris a matsayin sabon shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Bauchi.

Sanarwar da ta fito ta hannun mai bai wa gwamnan shawara kan sha’nin yaɗa labarai, Mukhtar Giɗaɗo, ta ce, “Gwamna Abdulkadir Bala Muhammed, ya aminta da naɗin sabbin masu ba shi shawara na musamman da kuma shugabannin hukumomin gwamnati na hukumomin da ba su da jagorori.”

Naɗin sabon sakataren ya zo ne tare da na wasu mutum biyar waɗanda aka naɗa a hukumomi daban-daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here