A Madina, Buhari ya yi addu’ar samun dawwamammen zaman lafiya a Nijeriya

0
108

A ziyarsa ya zuwa ƙasar Saudiyya, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara birnin Madina inda ya gabatar da sallolin Magriba da Isha.

A yayin sallolin, Buhari, tare da tawogarsa, sun yi addu’a mai yawa domin samun dawwamammen zaman lafiya a Nijeriya da ma duniya baki ɗaya.

Tun farko, bayan da ya isa babban filin jirgin sama na Yarima Muhammad Abdulaziz a Madina, Mataimakin Gwamnan yankin, Yarima Sa’ud Al-Faisal ne ya tarbi Buhari, inda suka kasance tare a Masallacin Annabi Muhammad, wuri na biyu mafi tsarki baya ga Masallacin Harami.

Shugaba Buhari da tawagarsa sun gabatar da salloli da karatun Alkur’ani, tare da yi wa Nijeriya da al’ummarta fatan alheri da lumana mai ɗorewa.

Haka kuma Shugaban Kasa Buhari da tawogarsa sun yi addu’a kan farfaɗowar tattalin arziƙi wanda ya shiga mawuyacin hali sakamakon annobar korona.

Ana sa ran da yamma Shugaba Buhari zai tafi birnin Makka domin gabatar da Ummara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here