NAHCON ta naɗa sabon sakatare, Kwantagora

0
512

Hukumar Hajji ta Nijeriya, NAHCON, ta naɗa Dakta Rabi’u Abdullahi Kwantagora a matsayin sabon sakataren ta.

Kwantagora ya samu gagarumar nasarar zama sakataren ne, inda ya zamto zakara a cikin mutane sama da 400 da su ka nemi wannan matakin.

NAHCON ta naɗa sabon sakataren ne bayan da ta bi hanyoyi daki-daki ta amfani da wasu kamfanunuwa masu u zaman kansu.

A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Shugabar Sashin Hulɗa da Jama’a ta NAHCON, Fatima Sanda Usara, mutane 448 ne su ka nemi wannan matsayin bayan da hukumar Hajjin ta tallata a manyan jaridu 3 na ƙasa, da su ka haɗa da Daily Trust, Blueprint da kuma Nations, inda a ciki kuma mutane 281 suka kai ga matakin tantancewa.

Daga cikin mutane 281 ɗin, 33 sun cika duk ƙa’idojin da a ke buƙata, inda hakan ya sanya a ka yi musu jarrabawa ta kafar yanar gizo inda 14 daga cikin su su ka samu nasara.

Sai a ka sake yiwa mutum 14 ɗin jarrabawa karo na biyu, inda 9 su ka samu nasara.

Daga bisani ne sai a ka yiwa mutane 9 ɗin jarrabawa ta tambayoyi baki-da-baki, inda 7 daga ciki su ka samu kaso 50 bisa 100 da kuma sama da haka.

Daga nan ne sai su waɗan nan kamfanunuwan masu zaman kan su da suka shirya jarrabawar su ka miƙa sunayen mutane 7 ɗin nan zuwa mahukuntan NAHCON.

Daga nan ne kuma NAHCON ɗin ta kafa kwamiti mai ɗauke da kwamishinoninta guda uku, inda a ka riƙa tantancewa har Dr Kwantagora ya zamo zakara.

A ƙarshe dai,Kwantagora, wanda ya ke da shaidar karatu ta digiri na uku, zai kama aiki ne a watan Nuwamba.

Haka kuma ya kasance ma’aikaci a hukumar alhazai ta birnin tarayya, Abuja tun daga shekarar 1995.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here