Shugaban Hukumar Alhazai ta Nassarawa ya taya sabon sakataren NHACON murna

0
421

Kwanaki biyu da naɗin sabon sakataren Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, Dr Rabi’u Abdullahi Kwantagora, saƙonnin murna da fatan alheri na ci gaba da zuba kamar ruwan sama daga masu ruwa da tsaki a harkar Hajji.

A wannan karon, Sakataren Hukumar Alhazai na Jihar Nasarawa, Malam Idris Ahmad Almakura ne ya bi sawun dandazon masoya wajen taya murna ga sabon Sakataren Hukumar Alhazai na Ƙasa, Dr. Rabi’u Abdullahi Kontagora.

Bayanin haka na ƙunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Alhaji Abdulrazaq Muhammad wadda kuma aka raba wa manema labarai a Lafia babban birnin jihar.

A cewar sanarwar, Idris Almakura ya nuna yaƙininsa kan cewa sabon sakataren NAHCON zai yi amfani da sanin da yake da shi wajen ciyar da hukumar da ma harkokin hajji na ƙasa gaba.

Haka nan, ya yaba wa kwamitin da ya yi aikin tantance waɗanda suka nemi wannan kujera wanda a ƙarshe Dr. Rabi’u Abdullahi Kontagora ya samu nasarar ɗarewa.

A ƙarshe, Idris Almakura ya ce yana da tabbacin cewa sabon sakataren zai taimaka wajen ba shi dukkanin goyon bayan da yake buƙata don ba shi damar cimma nasara a ayyukansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here