Mahajjatan da su ka fito daga Jihar Kaduna, waɗanda haɗarin ƙarfen ginin da a ke yi a harami ya rutsa da su yayin Hajjin 2015, sun koka kan cewa har yanzu ba su samu diyyar da Ƙasar Saudiyya ta bayar ba.
A bana, shekaru shida kenan da aukuwar wannan haɗari wanda ya yi sanadiyar mutuwar mahajjata da daman gaske.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, mummunan haɗarin ya auku ne a ranar 11 ga Satumban 2015, inda na’urar ɗaga ƙarfe mai nauyi da kayayyakin gini ta rikito kan mahajjata a Ka’aba a birnin Makka yayin da ake tsaka da ruwan sama wanda hakan ya yi ajalin mahajjata da yawa.
Mahajjatan Nijeriya shida ne suka rasu a haɗarin da suka fito daga jihar Gombe da Katsina da kuma Kaduna, yayin da mahajjata uku suka samu rauni.
Sai dai sahihan bayanai sun nuna cewa, Saudiyya ta saki kuɗaɗen diyyar waɗanda suka rasu da waɗanda suka jikkata a haɗarin tun a 2018.
A bayaninta, Saudiyya ta ce tana sa ran mahajjatan da suka ji rauni, kowannensu ya samu diyyar milyan N26.5, sannan ‘yan’uwan waɗanda suka rasu su samu milyan N53.1 ga kowanne.
Zubairu Adamu, wanda ɗan’uwa ne ga ɗaya daga cikin mahajjatan da suka rasu a haɗari mai suna Shuaibu Adamu daga ƙaramar hukumar Kubau, da kuma wani alhaji da ya samu rauni a kafaɗarsa, Ibrahim Sani, baki ɗaya sun yi kira ga Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da ya shigo cikin lamarin.
Zubairu ya shaida wa manema labarai cewa ɗan’uwansa ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya goma wanda har yanzu ba su samu diyyar mahaifinsu ba.
Sani ya ce sun rubuta wasiƙu don tunatarwa kan lamarin ga Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna da uwar goyonta ta ƙasa NAHCON, amma duk hakan bai haifar da wani ɗa mai ido ba.
Sa’ilin da aka tuntuɓe ta kan batun, shugabar riƙo ta Hukumar Alhazan Kaduna, Hajiya Hannatu Zaiýlani, ta ce cekin kuɗin da hukumar ta samu daga NAHCON a 2018, na ɗauke ne da sunan marigayin maimakon na magajinsa.
Daga: Daily Trust