Hukumar Alhazai ta Birnin Tarayya (FCT), ta nuna godiyarta ga ɗaukacin masoyan da suka nuna farin cikinsu gami da taya murna ga sabon Sakataren Hakumar Alhazai na Ƙasa (NAHCON), Dr. Abdullahi Rabi’u Kontagora.
Sanarwa manema labarai da hukumar ta fitar mai ɗauke da sa hannun Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Malam Muhammad Lawal Aliyu, ta nuna yadda Daraktan Hukumar Alhazai na FCT, Malam Muhammad Nasiru Danmallam da ɗaukacin ma’aikatan hukumar suka yi farin ciki dangane da irin saƙonnin taya murnar da masoya suka kwararo kan sabon sakataren.
A cewar Daraktan, “Haƙiƙa kalamai kaɗai ba za su wadatar ba wajen auna farin cikinmu dangane da wannan sabon muƙami, kuma muna da tabbacin cewa sabon sakataren zai ci gaba da yin aikinsa na samar da ci gaba a harkokin Hajji a matakin ƙasa musamman ma duba da irin sanin da ya tara a hukumar alhazai ta Abuja.
“Don haka muke fata tare da addu’ar Allah Ya sa sabon muƙamin Dr. Abdullahi Rabi’u Kontagora ya zama tsanin cigaba ga fannin Hajjin Nijeriya.
Daraktan ya ci gaba da cewa, samun wannan matsayi Dr. Rabi’u bai zo da mamaki ba ga ma’aikatar hukumar bisa la’akari da irin nasarorin da ya samu a bakin aiki a hukunar alhazai ta FCT.
Don haka ya ce suna da yaƙinin cewa da wannan sabon muƙamin nasa, fannin Hajji na Nijeriya zai ci gaba da samun bunƙasa.
“Yayin da muke miƙa godiyarmu ga dukkan waɗanda suka yi taya murna tun bayan sanar da naɗin da NAHCON ta yi, za mu ci gaba da yi masa fatan yin wa’adi mai cike da nasarori tare da neman haɗin kansa wajen samun kyakkyawar mu’amalar aiki tsakanin hukumar da dukkanin ruwa da tsaki a harkar Hajji na matakin ƙasa da na duniya baki ɗaya.
“Haka nan, muna kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a fanni Hajji da su ci gaba da bai wa hukumar cikakken haɗin kan da take buƙata don ci gaban harkokin Hajji”, in ji Danmallam.