*Martani: “Bayan shekaru 6, alhazan da haɗarin ƙarfen ginin Harami ya rutsa da su ba su samu diyya ba”*

0
301
ZIKRULLAH NAHCON CHAIRMAN

*Martani: “Bayan shekaru 6, alhazan da haɗarin ƙarfen ginin Harami ya rutsa da su ba su samu diyya ba”*

Daga Fatima Sanda Usara

Hankalin Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ya kai kan wani labari da jaridar Daily Trust ta buga a ranar Laraba, 3 ga Nuwamban 2021 mai taken, “Bayan shekaru 6, alhazan da haɗarin ƙarfen ginin Harami ya rutsa da su ba su samu diyya ba.”

A cewar labarin, wasu mutum biyu da suka yi iƙirarin haɗarin ya shafe su, sun nemi gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i ya shigo cikin lamarin bayan da suka rubuta wasiƙa zuwa ga Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna da kuma Hukumar NAHCON, “amma hakan bai haifar da ɗa mai ido ba.”

Haka nan, an nuna ɗaya daga cikin masu ƙorafin ɗan’uwa yake ga alhajin da ya rasa ransa, yayin da gudan kuma ya ji rauni sakamakon haɗarin.

Lallai NAHCON ta samu wasiƙu daga hannun wasu da haɗarin ya shafa daga jihar Kaduna, wanda kuma hukumar ta maida musu da amsar wasiƙun nasu. Kuma an sanar da wanda ya yi iƙirarin cewa ya ji rauni a haɗarin cewa, Saudiyya ta biya diyya ne kaɗai ga waɗanda suka ji munanan raunuka, kuma Saudiyyar ce da kanta ta kwashe su zuwa asibiti.

Amma waɗanda raunukansu ba su tsananta ba, an ɗauki matakin kula da su ne kyauta a asibitin Saudiyya ba tare da biyan su wata diyya ba, faƙat. Don haka, an sanar da shi sunansa ba ya cikin waɗanda Masarautar Saudiyya ta miƙo cekin kuɗinsu .

Dangane da ko ina kuɗaɗen diyyar suka shige? Idan za a iya tunawa, a ranar 9 ga Disamban 2019 hukumar NAHCON ta bada bayanin cewa Masarautar Saudiyya ta saki diyyar alhazan da haɗarin ƙarfen gini ya rutsa da su a 2015 ga ofishin jakadancin Nijeriya da ke birnin Riyadh, kuma ofishin zai tura diyyar ga hukumar don jan ragamar biyan diyyar ga waɗanda suka dace bayan kammala dukkan tsare-tsare a Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya wanda kuma an samu kammala tsare-tsaren.

Sai dai kash! Cekin kuɗin da NAHCON ta karɓa an samu matsaloli guda biyu. Da farko, cekin kuɗaɗen na ɗauke ne da sunayen waɗanda suka rasu a haɗarin, sannan abu na biyu da Dalar Amurka aka bada cekin ga waɗanda lamarin ya shafa.

Wannan ya sa NAHCON ta rubuta wa Babban Bankin Nijeriya (CBN) takarda tana mai neman bankin ya ɗora ta a hanyar da ta dace kan yadda za ta biya cekin Dalar Amurka da ta karɓa ga masu haƙƙi ta hannun gwamnonin jihohinsu.

Amma sai CBN ya amsa da cewa, babu halin karɓar cekin Saudiyya a kowane bankin Nijeriya. Don haka CBN ya bada shawara kan cewa, sai dai ana iya biyan kuɗaɗen ta cikin asusun NAHCON da ke CBN kafin daga nan a samu a fitar da kuɗin a biya masu haƙƙi haƙƙoƙinsu.

A bisa wannan shawara ta CBN ne NAHCON ta rubuta wa ofishin jakadancin Nijeriya da ke Riyadh takarda a hukumance inda ta buƙaci ofishin ya haɗa kai da duk hukumomin Saudiyya da suka dace don a samu a saka kuɗaɗen cikin asusun NAHCON.

Kuma an yi sa’a Ofishin Jakadancin ya amsa kira ta hanyar sanar da Ma’aikatar Harkokin Waje ta Nijeriya da hukumar NAHCON, wanda a halin da ake ciki duka ɓangarorin na zaman jiran mataki na gaba da za a ɗauka a kan batun.

Lamarin bai yi daɗi ba ganin yadda jaridar Daily Trust ta yi hanzarin fitar da labari ba tare da ta nemi ji daga duka ɓangarorin da abin ya shafa ba.

Wannan marubucin ya ga alamar kiran da wakilin Daily Trust a NAHCON ya yi da misalin ƙarfe bakwai na dare saura mintuna uku kafin fitar da rahoton nasu, har ma da ƙarin saƙon tes da misalin ƙarfe 7:22 na dare inda ya nemi jin ta bakin NAHCON dangane da biyan diyyar waɗanda suka mutu a haɗarin ƙarfen ginin Harami da ya rikito a shekarar 2015 wanda aka amsa da za a bincika sannan a bada ba’asi, kuma marubucin ya amsa da madalla.

Yanzu ya tabbata cewa da ma jaridar ta riga ta gama rubuta labarin ‘yan sa’o’i kafin ta shiga maɗaba’a. Maimakon yin cikakken bincike sai aka ɓuge da neman hujja a takurarren lokaci wanda ba za a iya samar da bayanan da ake buƙata duka ba nan take.

Kada aikin jarida ya tsaya a kan son bada labarai da ɗumi-ɗuminsa, akwai sauran abubuwan lura da dama da suka haɗa da yi wa labari adalci, tabbatar da cewa labari ba zai haifar da wani cikas ko barazanar tsaro ga waɗanda labarin ya shafa ba bayan an fitar da shi, misali kamar dai waɗanda samun diyyar ya shafa.

Jaridar ta ambaci maɗuɗun kuɗaɗe a matsayin kason da ‘yan’uwan waɗanda lamarin ya shafa za su samu ba tare da yin la’akari da irin ƙalubalen tsaron da ake fuskanta ba a wannan lokaci, shin ina wayewa a cikin haka?

Domin ƙarin haske, Saudiyya ba ta bada kuɗaɗen diyyar duka alhazan da suka mutu da waɗanda suka ji rauni wuraren 2018 ba kamar yadda jaridar ta ce ta tattaro.

_Fatima Sanda Usara ita ce shugabar Sashen Hulɗa da Jama’a na Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON)_

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here