Hukumar Kula da Alhazai Musulmai za ta ƙulla alaƙar aiki da ta Alhazai Kiristoci a Bauchi

0
500

A wani yunƙuri na ƙarfafa alaƙar aiki, Sakataren Hukumar Alhazai na Jihar Bauchi, Imam Abdurrahman Ibrahim Idris, ya yi na’am da ƙulla alaƙar aiki mai ƙarfi tsakanin hukumarsa da takwararta mai kula da alhazai Kiristoci a jihar.

Imam Abdurrahman ya bayyana amincewarsa ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Sakataren Hukumar Kula da Alhazai Kiristoci na Jihar, Hon. Samuel J. Haruna, a ofishinsa a ranar Laraba.

Imam Abdurrahman ya bayyana hukumomin biyu a matsayin tagwayen hukumomi waɗanda ke ɗauke da nauyin kula da jin daɗi da walwalar alhazai a jihar.

Sanarwar manema labarai da ta fito ta hannun jami’in labarai na hukumar, Muhammad Sani Yunusa, ta nuna Imam Abdurrahman ya yaba da irin goyon bayan da gwamnan jihar, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad, yake bai wa tagwayen hukumomin domin ganin sun yi nasara a harkokinsu.

Daga nan, ya bai wa gwamnan tabbacin yin bakin ƙoƙarinsu wajen bai wa maniyyatan jihar kulawar da ta dace. Kana, ya buƙaci da a wanzar da ingantacciyar alaƙa a tsakanin hukumomin biyu.

A nasa ɓangaren, sakataren hukumar kula da maniyyata Kiristoci, Samuel J. Haruna, ya ce dalilin ziyarar shi ne, don taya Imam Abdurrahman Ibrahim Idris murnar sabon matsayin da ya samu na Sakataren Hukumar Alhazai, tare da nuna buƙatar da ke akwai na haɗin kai don yin aiki tare.

A hannu guda, Imam Abdurrahman Ibrahim Idris ya samu ganawa da jami’an harkokin hajji daga ƙananan hukumomi 20 da jihar Bauchi ke da su a babban zauren taron hukumar.

Imam ya yi kira ga jami’an da su bai wa ayyukansu muhimmanci don tabbatar da nasarar a ayyukan Hajji. Tare da nusar da su kan cewa su sani, galibin maniyyatan jihar daga ƙauyuka suke fitowa waɗanda ke da ƙarancin ilimin amfani da kafofin sadarwa na zamani da kuma abubuwan da suka shafi Hajji.

A ƙarshe, ya bayyana yaƙininsa kan cewa, jami’an Hajji na ƙananan hukumomin za su bada cikakkiyar gudunmawarsu wajen faɗakar da maniyyatan jihar da kuma taimakawa wajen samun aikin hajji mara cunkoso don bai wa maniyyata aiwatar da aikin Hajji karɓaɓɓe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here