Malaysia za ta bayyana kuɗin kujerar Hajji a farkon shekarar baɗi

0
363

Mataimakin Minista a ofishin Firaminista, ɓangaren harkokin addini a Malaysia, Datuk Ahmad Marzuk Shaary, ya bayyana cewa, ana sa ran bayyana kuɗin kujerar Hajji kafin farkon shekarar baɗi.

Sai dai Ahmad bai bada tabbcin cewa ba za a samu ƙari a kuɗin hajjin ba duba da cewa Gwamnatin Saudiyya ma za ta ɗaga harajin kayayyaki da ta saba karɓa da kashi 15 cikin 100.

A cewarsa, “Ana sa ran farashin ya ƙaru duba da sabbin tsare-tsaren da aka gabatar don yaƙi da annobar korona.”

Marzuk ya shaida wa manema labarai a ranar Talatar da ta gabata cewa, “Za a bayyanar da tsayayyen farashin tafiya hajjin ne bayan kwamitin zartarwa sun gana nan da farkon shekara mai zuwa.”

Kafin wannan lokaci, an ruwaito cewa ana sa ran farashin zuwa hajji zai ƙaru, lamarin da aka danganta shi da dokar bada tazara a tsakani, kamar a wuraren da suka shafi masaukin baƙi da cikin motocin jigilar alhazai da kuma abin da ya shafi taƙaita zirga-zirgar mahajjata a cikin Masallacin Harami.

Kodayake dai Ahmad Marzuk ya ce, gwamnati za ta ci gaba da bada tallafi ga waɗanda ke da niyyar zuwa Hajji.

“Kafin ɓullar annobar korona, farashin kujerar Hajji kimanin RM24,000 ne, amma RM9,980 kacal ake buƙatar kowane maniyyaci ya biya, yayin da gwamnati ke ɗaukar nauyin biyan cikon kuɗin”, in ji Marzuk.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here