Jordan ta gana da Saudiya a kan Ummara

0
292

Ministan Harkokin Addinin Musulunci da Gurare masu tsarki na Jordan, Dr. Mohammad Khalayleh, ya gana da Ministan Hajj da Ummara na Saudi Arebiya, Dr. Tawfiq Rabiah, a kan haɗin gwiwa da kuma tsare-tsare da za a yi ƴan ƙasar Jordan ɗin su zo Ummara ta ƙasa da kuma ta jirgin sama.

Da ya ke bayani bayan ganawar, Kahalayleh ya jaddada ƙarfin haɗin gwiwa da abota tsakanin Saudiya da Jordan wanda hakan ya faru ne sakamakon hikima daga shugabancin ƙasashen biyu da kuma son ƙarfafa danƙon zumunci.

Ya ƙara da cewa hukumar kula da harkokin addinin za ta sanar da shirye-shiryen ta na Hajjin 2022 bayan da Saudi ta gama karantar yanayin ta kuma fitar da matsaya, inda ya bayyana ƙarin gwiwar sa cewa za a yi Hajji a shekarar bayan da annobar korona ta kawo cikas.

A nashi ɓangaren, Rabi’ah ya yabawa shugabancin Jordan ɗin inda ya jaddada cewa a shirye Saudiya ta ke wajen ƙarfafa ƙawance da haɗin gwiwa mai ƙarfi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here