Kwamishina a NAHCON ya kai ziyarar duba yanayi a ofishin hukumar Hajji na kudu-maso-kudu

0
311

Kwamishinan sashin tsare-tsare, bincike, ƙididdiga, bayanai da ma’ajiyar bayanai (PRSILS) na Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, Sheikh Prince Suleman Momo, na a Port Harcout domin ziyarar aiki ta kwanaki 3 zuwa ga ofishin hukumar na kudu-maso-kudu.

Ya kai ziyarar ne domin duba yanayin gine-gine da ofisoshin Hukumar a yankin, haka shima Kwamishina mai kula da shiyyar kudu-maso-kudu, Alhaji Sadiq Kusa tare da jami’in tsare-tsare na shiyya, Alhaji Aminu Ukoha tare da shugabannin hukumomin alhazai na shiyyar ne su ka tarbi tawogar kwamishinan.

Kwamishinan zai gana da shugabannin hukumomin alhazai na shiyyar, secretary da kuma ma’aikatan hukumar na shiyyar ne su ka tarbi kwamishinan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here