Za a fassara fatawoyin Shari’a a harshen Hausa, Turanci, faransa da sauransu a Harami

0
382

Babban Ofishin Kula da Masallatan Harami Guda Biyu, wanda ofishin gudanarwa da shawarwari ya ƙaddamar da wani aiki na fassara tambayoyi da su ka shafi shari’a a yarurruka bakwai na ƙasashen waje domin alhazan Ummara da kuma masu ziyara zuwa Harami.

Shirin, wanda a ka yi wa laƙabi da “za mu sa ku a hanya da yaren ku”, ya ƙunshi yarurruka da su ka haɗa da turanci, Urdu, Persian, French, Turkish, Hausa da Bengali.

Babban Ofishin ya tanadi wani tsari na samar da mafassara a wasu gurare domin taimakawa duk wanda ya ke da wata tambaya da ta shafi shari’a da kuma aikin ibada.

Alhazai da masu ziyara za su samu amsoshin tambayoyin su da harshen Yaren su.

Manhajar ta ƙunshi wani mutum-mutumi, ko ta na’urar sadarwa ta allo mai hoto ko kuma wayar sadarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here