Ma’aikata 4,000 za su riƙa amfani da lita 45,000 ta turare domin tsaftace Masallacin Harami sau 10 a rana

0
373

Masallacin Harami na Makka na shan tsaftacewa bayan da a ke goge shi da sinadaran kashe ƙwayoyin cuta sau 10 a rana, Saudi Press Agency ce ta rawaito.

Ma’aikata 4,000 ne maza da mata su ke aikin goge-gogen inda aka naɗa manyan ma’aikata 200 suna duba aikin da su ke yi.

Haka kuma an sanya na’urar feshi guda 100 inda za su riƙa feshin turare mai yawan lita 45,000 a harabar masallacin.

Na’urori 500 ne da sauran injina a ka girke domin yin wannan hidimar, inda kowacce na’ura za ta riƙa yin minti 25 domin tabbatar da cewa ba a takurawa masallata ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here