Ƴan ƙasashen waje ka iya neman zuwa Ummara ta manhajojin wayar salula- Saudiyya

0
146

Saudi Arebiya ta bayyana cewa, daga yanzu maniyyata daga ƙasashen ƙetare za su iya neman izinin yin Ummara da yin salloli a Masallacin Harami na Makka, danka kai ziyara zuwa Masallacin Ma’aiki a Madina ta hanyar amfani da sabuwar manhajar wayar salula da aka samar da ita don buƙatar hakan.

Ma’aikatar Hajji da Umurah ta Saudiyya tare da haɗin gwiwar hukumar Saudi Data & Artificial Intelligence Authority (SDAIA) suka fitar da wannan sabuwar hanya don amfanin maniyyata.

Ma’aikatar ta ce, daga yanzu maniyyata baƙi kamar mazauna masarautar Saudiyya za su iya amfani da manhajar Eatmarna da ta Tawakkalna wajen yin bukin tafiya da kuma ziyarar zuwa Masallatai biyu masu alfarma.

Ta ƙara da cewa, masu neman izini na ‘permits’ wajibi ne su soma da yin rijista a dandalin nan na ‘Saudi Quddum’ don samun damar yin amfani da manhajar Eatmarna da ta Tawakkalna.

Don haka ma’aikatar ta shawarci matafiya kan su sauke waɗannan manhaja a kan waoyinsu kafin zuwa masarautar Saudiyya.

Ta ce, ilahirin filayen jirgin saman ƙasar suna aiki cikakke kamar yadda lamarin ya ke a can baya biyo bayan sabbin tsare-tsaren da hukumar sufurin jiragen sama ta ƙasar ta ɓullo da su a watan Oktoban da ya gabata.

Hukumomi ƙasar sun yi kira ga masu amfani da waɗannan manhajojin da su riƙa sabunta su ta amfani da rumbun manhaja na Apple ko Google stores, ko Huawei App Gallery da kuma Galaxy Store a wayoyin android.

A watan Agustan da ya gabata ne Saudiyya ta buɗe hanya don bai wa maniyyatan ƙetare da suka yi allurar rigakafin korona damar zuwa yin hajjin Umurah bayan ta rufe iykokinta sakamakon annobar korona.

Ma’aikatar ta ce, farali ne maniyyata su mallaki shaidar rigakafin korona kafin samun izinin yin Umurah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here