Ƙungiyar wayar da kan alhaxai fulani ta ziyarci shugaban hukumar Hajji ta Taraba

0
373

Shugabannin Ƙungiyar Wayar da Kan Fulanin Nijeriya Maniyyata reshen Jihar Taraba, sun kai ziyarar aiki ga Sakataren Hukumar Alhazai na jihar, Alhaji Umar Ahmed Chiroma.

Da yake jawabi yayin ziyarar, shugaban ƙungiyar na jiha, Alhaji Isma’ila Musa ya ce, manufar ƙungiyar shi ne wayar da kai da kuma ilimantar da Fulani maniyyata wanda a cewarsa, su ke samar da kashi 70 na maniyyatan Nijeriya.

Shugaban ya ƙara da cewa, daga cikin kashi 70 na Fulani maniyyatan kusan kashi 60 ba su da ilimin ibada da na mu’amala da ake buƙata game da aikin Hajji.

Don haka ya ce wannan ne ya haifar da buƙatar assasa wannan ƙungiya ta musamman wadda za ta faɗakar da Fulanin cikin harshen da suka fi fahimta.

A nasa ɓangaren, Sakataren Hukumar Alhazai na Jihar Taraba, Alhaji Umar Ahmed Chiroma, ya yi alƙawarin yin aiki tare da ƙungiyar musammam ma a lokutan ayyukan Hajji. Kana a ƙarshe, ya yaba wa ƙungiyar da kuma ƙoƙarinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here