Gwamna Bala ya naɗa sabon mai ba shi shawara kan alhazai

0
436

Gwamnan jihar Bauchi, Alhaji Bala Abdulƙadir Muhammad ya naɗa, Alhaji Adamu Madaki a matsayin sabon mai bashi Shawara kan harkokin alhazai.

A jiya Talata ne dai Madaki ɗin ya kama aiki, tare da alƙawarin cewa zai bada gudunmawa wajen gudanar da harkar Hajji a jihar Bauchi.

Ya baiyana hakan ne a wani ɗan takaitaccen taro da ya yi a lokacin da ya kama aiki a sabon ofishin na sa.

Alhaji Madaki ya yi alƙawarin zai yi aiki tare da haɗingwiwar ma’aikata da shugabannin hukumar alhazai ta jihar, in da yai kira gare su da suka su bada gudunmawa mai yawa domin ci gaban Hajji a jihar.

Tun da fari, babban sakataren hukumar, Imam Abdurrahman Ibrahim ya taya Madaki murnar muƙamin nasa sannan yai masa fatan alheri.

Ya kuma yi kira ga ma’aikatan hukumar da su baiwa Madaki ɗin haɗin kai domin ya dauke nauyin da gwamnan jihar ya ɗora masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here