Sabon babban mai bawa gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad shawara kan harkokin aikin Hajji Alhaji Adamu Madaki ya karɓi ragamar aiki a yau Laraba 16th ga watan Nuwamban wannan shekara ta 2021, tare da shan alwashin bada gudumawarsa wajen kawo ci gaba a ɓangaren harkokin aikin Hajji a jihar Bauchi.
Alhaji Adamu Madaki ya bayyana haka ne a yayin da gudanar da ƙwarya ƙwaryar bikin miƙa rahoton Kama aiki, wanda ya gudana a ɗakin taro na hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar Bauchi.
Babban mai bada shawarin ya kuma yi alƙawarin yin aiki tare da hukumar gudanarwa da ɗaukacin ma’aikatan hukumar,kana ya buƙacesu da su bashi dukkan haɗin kai da ya kamata domin samun sanarar gudanar da aikinsa yanda ya kamata.
Sai ya yi amfani da wannan dama wajen shawartar illahirin ma’aikatan hukumar da su maida hankali tare da sadaukar da kansu a bakin aiki kamar yanda hukumar kula da ma’aikatan Gwamnati ta tanadar.
Tun farko a jawabinsa na maraba da baƙi, Babban sakataren Hukumar jin daɗin Alhazai na jihar Bauchi Imam Abdul-Rahaman Ibrahim Idris,taya murna ya yiwa babban mai bada shawarin bisa bashi muƙamin,gami da yimasa addu’ar Allah ya bashi Nasarar gudanar da aikinsa.
Da yake nuna ƙwarin guiwarsa kan sabon babban mai bada shawarin, Imam Abdul-Rahaman ya yi kira ga ma’aikatan hukumar da su bashi dukkan haɗin kan da ya kamata domin ƙara masa ƙarfin guiwar sauke nauyin da gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad ya ɗora masa.
Muhammad Sani Yunusa
Jami’in Watsa Labarai