Tunisia za ta yi wa maniyyata 195,000 rijistar Hajjin 2022

0
704

Ministan Harkokin Addinai na Tunisia, Ibrahim Chaibi ya baiyana cewa za a yi wa maniyyata 195,000 rijistar Hajji 2022 kafin Saudi Arebiya ta fitar da adadin mahajjatan da za su yi aikin Hajjin.

Ya ƙara da cewa a ranar Lahadi ne ma za a rufe yin rijistar, inda a ka samu adadin maniyyata 195,000.

A wata sanarwa da ya fitar, Chaibi ya ƙara da cewa har yanzu Tunisia na tsimayen bayani kan adadin alhazan da za su je aikin Hajjin 2022 daga Saudi Arebiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here