Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Jihar Bauchi Ta Nemi Ƙwaƙƙwarar Haɗin Kai Da Kafofin Watsa Labarai

0
456

Hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar Bauchi ta buƙaci ƙwaƙƙwarar haɗin guiwa da kafafen yaɗa labarai, domin samun damar gudanar da nagartaccen aiki ga maniyata na jihar.

Babban sakataren Hukumar Imam Abdul-Rahaman Ibrahim Idris, shiya yi wannan kira a yayin da ya karɓi baƙwancin tawagar hukumar gudanarwa ta Albarka Radio da ta ziyarce shi a ofishinsa,ya ce “aiki da kafafen watsa labaran abune da yafi kamata a bawa fifiko”.

Imam Abdul-Rahaman ya kuma yabawa kafafen yaɗa labarai bisa kishin da suke nunawa na ƙoƙarin wayarda kan al’umar jihar Bauchi, bisa kyawawan tsare-tsare da shirye-shiryen gwamnatin Bala Abdulƙadir Muhammad,tare da yin kira garesu da su ɗore akan hakan.

Ya ƙara da cewa hukumarsa ta shirya tsab domin fara gudanar da shirye-shirye na musamman a kafafen watsa labarai dangane da gudumawar gwamnati na samarda walwala da jin daɗin Alhazai na jihar Bauchi,sai ya yi kira ga kafafen yada labarai da su ci gaba da bada tasu gudumawar wajen isarda kyawawan labari na hukumar ga al’uma.

Tun farko da yake nasa jawabin shugaban Albarka Radio Alhaji Dauda Muhammad Chioma, ya bayyana cewar gidan Redi’on zai cigaba da yin aiki tare da hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar Bauchi, tare da nuna buƙatar ɗorewar kyakkyawar dangantakar dake tsakaninsu wajen yin aiki tare.

A wani labari makamancin wannan ƙungiyar haɗaka da tabbatar da adalci a Arewa da samarda nagarta wato The Organization, Coalition Arewa Justice and Integrity a turance ta ziyarci babban sakataren a ofishinsa.

Da yake gabatarwa babban sakataren hotonsa mai ɗauke da kwanan wata da saƙon taya murna, Shugaban ƙungiyar na ƙasa Yusuf Tanko, ya ce maƙasudin ziyarar itace, domin taya babban sakataren murnar samun kujerar, bisa cancantarsa da gwamna Bala Abdulƙadir Muhammad ya gani tare da yi masa fatar Alkhairi.

Da yake maida jawabi babban sakataren Hukumar jin daɗin Alhazai na jihar Bauchi Imam Abdul-Rahaman Ibrahim Idris bayyana ziyarar ya yi a matsayin kara da suka masa,a kuma alokacin da ya dace,gami da yin alƙawarin samar da dai daito aduk halinda ya tsinci kansa.

Muhammad Sani Yunusa
Jami’in Watsa Labarai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here