Mu na daf da fara jigilar alhazan Ummara- Hukumar aljazan Katsina

0
356

Hukumar Alhazai ta Jihar Katsina ta bayyana ƙudinrinta na yin amfani da babban filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua wajen soma jigilar alhazan Umurah na jihar zuwa ƙasa mai tsarki.

Hukumar ta ce ta yi wannan ƙudiri ne bayan da ta samu amincewar Gwamnan Jihar kan ta soma harkokin Umurah.

Daraktan Gudunarwa na Hukuma,Alh. Suleiman Nuhu Kuki, shi ne ya yi waɗannan bayanai yayin wata ganawa da suka yi tare da hukumar kula da Babban Filin Jirgin Sama na Umaru Musa Yar’adua a hedikwatar hukumar da ke Katsina.

Kuki ya shaida wa hukumar filin jirgin saman cewa Gwamnan Jihar ya amince wa Hukumar Alhazan ta soma harkar Umurah, kuma hukumar ta yanke shawarar ta yi amfani da Filin Jirgin Saman Umaru Musa Yar’adua wajen jigilar maniyyatan jihar.

Sanarwar da ta sami sa hannun Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Alh Badaru Bello Karofi, ta ce Daraktan Hukumar ya sanar da su a hukumance aniyyar da hukumar ke da ita ta soma jigilar Alhazan Umurah rukunin farko ya zuwa Janairun 2022 da ma watan Ramadan mai zuwa lokacin da aka fi zuwa Umurah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here