Muna da yaƙinin za a yi Hajji a 2022- Maniyyatan Delta

0
36

Yayin da gwamnatin Saudiya ke cire matakan kariya daga kamuwa da korona daki-daki, maniyyata a Nijeriya na sa ran za a yi Hajjin 2022 lami lafiya.

Wasu Musulmai a Warri, Jihar Delta sun nuna ƙwarin gwiwarsu cewa za su je Hajjin na baɗi.

Gwamnatin Nijeriya dai na fatan cewa maniyyatan ta za su je Hajjin baɗi bayan da ƙasar Saudi Arebiya ta soke yin Hajji ga ƙasashen waje tsawon shekaru biyu da su ka gabata.

Wasu maniyyata daga Delta na farin ciki da cire matakan korona ɗin da Saudiya ke yi kuma su na fatan za su je su yi ibadar a baɗi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here