Saudiya ta soke ƙaiyade shekarun alhazan Ummara

0
572
FIRST BATCH 2020 PILGRIM

Saudi Arebiya ta soke ƙaiyade shekarun alhazan Ummara da za su zo daga ƙasashen waje, inda hakan ke nufin cewa ƙasar ta bari a riƙa bada takardar sahalewa da kuma ajiye gurbin zuwa Ummara tsofaffin da za su zo Ummara da ga ƙasashen waje.

Saudiya ta bar waɗanda ba masu Ummara ba su yi ɗawafi a filin ka’aba.

A baya dai Ma’aikatar Hajji da Ummara ta sanya shekaru 18 zuwa 50 ga waɗanda za su zo Ummara da ga ƙasashen waje.

Amma a yanzu, sai ma’aikatar ta soke shekaru 50 ɗin na zuwa Ummara, amma ba ta soke shekaru 18 da ƙaiyade na zuwa Ummara ba.

Hakan na nufin dole sai alhajin Ummara ya cika shekara 18 sannan za a bashi damar zuwa Ummara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here