Ƴar kasuwar da a ka kama da ƙwaya za ta tafi Saudiya ta kasayar da ɗauri 80 na hodar iblis

0
134

Jami’an Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Ƙwayoyi, NDLEA sun cafke wata mata a kan hanyarta ta zuwa Jidda, Saudi Arebiya domin yin Ummara.

An kama matar, wacce ƴar kasuwa ce, a filin jirgin sama na Nnamdi Azikuwe bayan da a ka gano cewa ta haɗiye ƙulli 80 na hodar iblis, wacce a ka fi sani da ‘cocain’.

A wata sanarwar da kakakin hukumar, Femi Babafemi ya saki a ranar Litinin, NDLEA ta ce matar, mai suna Adisa Afusat Olayinka, ƴar shekara 46 na zaune ne a Ibafo, Jihar Ogun sannan ta tashi a Ƙaramar Hukumar Ilori ta gabas a Jihar Kwara.

Sanarwar ta ce an kama matar ne a yayin tantance matafiya a kan layin shiga jirgin Qatar Airways 1418 a ranar Laraba, 24 ga Nuwamba.

“Da ga nan sai a ka kaita shelkwata in da ta kasayar da ɗauri 80 na hodar iblis tsakanin Laraba zuwa asabar ta watan da mu ke ciki,” in ji kakakin.

A yayin da a ke tuhumar ta, in ji Babafemi, Olayinka ta ce ta tara kuɗi har miliyan 2.5 a tsawon shekara ɗaya inda daga bisani ta riƙa siyan ƙwayoyin a tsitstsinke a gurare 6 a yankin Mushin a Jihar Legas.

” Ta kuma baiyana mana cewa tana sayar da kayan sawa daga baya yanci bashin Naira miliyan ɗaya a wajen mutane uku har ya haɗa kuɗin da ta sayi ƙwayar nan. Ta ƙara da cewa ta kashe miliyan ɗaya wajen sabunta fasfo ɗin ta.

“Ta ce wata mata da ta haɗu da ita a yayin wata tafiya da ta yi zuwa Saudiya a 2019 itace ta ƙarfafa mata gwiwar aikata wannan lafiin.

“ta ce wai tana son tara miliyan 7 je domin ai mata aiki a mahaifarta saboda shekarar ta 28 da yin aure amma bata taɓa haihuwa ba kuma mutane suna ta damun ta da surutu,” in ji Olayinka.

Bayan ya yabawa jami’an bisa wannan jan aiki da su ka yi, shugaban hukumar na ƙasa, Buba Marwa ya ja hankalin su kan su sanya ido a kan gano masu safarar ƙwaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here