IHR ta buɗe sabuwar jaridar yanar gizo, The Target News

0
452

Ƙungiyar Masu rahoton harkokin Hajji da Ummara Mai Zaman Kan ta, IHR, wacce ta ke kawo rahotanni da ga Najeriya da Saudi Arebiya, ta samar da sabuwar jaridar yanar gizo mai suna THE TARGET NEWS.

Wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mawallafinta, Ibrahim Muhammad ta ce sabuwar jaridar za ta mayar da hankali wajen yaɗa labaran da su ka shafi kowanne ɓangare da su ka haɗa da Siyasa, tattalin arziki, tsaro, sadarwa, noma da sauransu.

“Za ta yi ƙoƙarin zama wani tushe na haɗin kan kasa”, inji sanarwar.

A cewar mawallafin jaridar, za a samu jaridar a shafinta na www.thetargetnews.com.ng , inda ya ƙara da cewa nan gaba kaɗan za a fara buga jaridar a takarda.

“Muna ƙoƙarin mu ga ta ci gaba ta haɗe dukka nau’o’in aikin jarida na Rediyo da Talabijin”

Acewar mawallafin, jaridar ta TARGET NEWS, babbar manufarta ita ce samar da zaman lafiya da samar da bayanai cikin yaruka da dama da labarai sahihai cikin yaraon da masu karatu za su fahimta.

Shugaban kamfanin jaridar ya ce “Jaridarsu ta farko wato Hajj Reporters Online za ta ci gaba da zama cibiyar samun labarai ta farko, tare da ilimantarwa da wayar da kai kan ayyukan Hajji da Umarah.

Kamfanin Hajj Reporters Media Ltd, shi ne ke wallafa jaridun Hajj Reporters, hajjreportershausa da Hajj Reporters Magazine tare kuma da sura sakon kar ta kwana kyauta ga kan batun aikin Hajj da Umrah ga sama da mabiya addinin musulunci dubu 5.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here