Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta yabawa Ƙasar Ghana bisa yadda ta ɗore wajen tallafawa Musulmai marasa ƙarfi a ƙasar.
A ƴan shekarun nan, gwamnatin Ghana na yin jigilar aikin hajji a farashi mai rahusa.
Shugaban NAHCON, Barista Zikrullah Kunle Hassan ya yabawa gwamnatin ƙasar, in da ya ce tsarin na da muhimmanci matuƙa, musamman ta yadda a ka cire shingen da ya ke hana musulmai zuwa aikin Hajji saboda rashin hali.
Hassan ya baiyana hakan ne yayin da kai ziyarar aiki zuwa Hukumar Hajji ta Ghana.
Hassan ya ƙara da cewa shi kuma tallafi da alhazan Nijeriya ke samu daga NAHCON ya ke zuwa ta hanyoyin jigilar alhazai, wasu shirye-shirye da ta ke ƙirƙira sai kuma aiyukan ci gaba da ta ke aiwatarwa.
” A na saka wasu kuɗaɗe a cikin kundin biyan aikin Hajji domin a samu damar yi wa alhazai hidima,” in ji shugaban NAHCON.
Ya kuma ƙara da cewa NAHCON na haɗin gwiwa da ƴan kasuwa domin yin kasuwanci da wasu kadarorin ta.