DA ƊUMI-ƊUMI: Saudiya ta rage adadin shekarun bada izinin Ummar daga 18 zuwa 12

0
525

Ma’aikatar Hajji da Ummar ta Ƙasar Saudiyya, ta ce ta rage adadin shekarun bada izinin zuwa Ummara daga 18 zuwa 12

Maikatar ta ƙara da cewa za ta baiwa yara ƴan shekara 12 zuwa sama damar zuwa Ummara daga kowace ƙasa, in dai sun yi rigakafin korona.

Sannan za su samu damar yin sallah a Harami da Rawdah Al Shareefah da kuma yin ziyara.

Kafar Haramain ta rawaito cewa, “An rage mafi ƙarancin shekaru na zuwa Ummara da ziyarar Masallatai biyu masu alfarma daga shekara 18 zuwa 12 da sama da haka ga kowace ƙasa”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here