Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da shigowar jirage daga Canada, Britaniya da Saudiya

0
319

A wani salo da za a iya cewa ramuwar gayya ce, da ga ranar 14 ga watan Disamba, Gamwantin Taraiya za ta dakatar da jirage da ga Canada, Britaniya da Saudi Arebiya da ga shigowa Nijeriya.

Ministan Harkokin Sufurin Jirgin Sama, Hadi Sirika ne ya sanar da hakan a yau Lahadi a Legas.

Sirika ya yi bayanin cewa gwamnati ta sanya takunkumin ne a matsayin ramuwa ga dakatar da jirage da ga Nijeriya da ƙasashen su ka yi sakamakon ɓullar sabon nau’in korona na Omicron.

Ya ƙara da cewa gwamnatin ƙasar nan za ta sanya waɗan nan ƙasashe ukun a matsayin waɗan da za a sanyawa idanu sakamakon ɓullar Omicron ɗin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here