Omicron: Dakatar da jirage da ga Nijeriya ba ya na nufin soke Hajji ba — Saudiya

0
83

Saudi Arebiya ta ce dakatar da jigilar jirage zuwa ƙasar bai shafi aikin Hajjin 2022 ba.

A tuna cewa a ranar Talata ne Maikatar Harkar Sufurin Jirgin Sama ta Saudiya ta dakatar da jirage da ga Nijeriya zuwa ƙasar a wani mataki na daƙile yaɗuwar sabon nau’in korona na Omicron.

Amma wata sahihiyar majiya daga ofishin jakadancin Saudiya a Nijeriya ta shaidawa jaridar The Guardian cewa ƙasar Saudiya ba ta da wata niyya ta soke, ko hana Nijeriya zuwa aikin Hajji.

Duk da cewa Saudiya ta soke Hajji ga ƴan ƙasashen waje a shekaru biyu da su ka gabata, majiyar ta shaidawa jaridar cewa har yanzu ƙasar ba ta fiida matsaya a kan Hajji ba.

“Saudiya na samar da duk wasu tsaruka na yaki da cutar korona domin kare ƴan ƙasa, baƙi da kuma alhazai. Sannan wannan dakatar da jiragen da ga Nijeriya na wucin-gadi ne kuma bai shafi Hajjin 2022 ba.

“Sabo da haka saɓanin yadda a ke ta raɗe-raɗi, Saudiya ba ta soke aikin Hajji ba,” in ji majiyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here