Sudais ya ƙaddamar da fasahar ganin dutsen Hajrul Aswad ta na’ura

  0
  141

  Shugaban Babban Ofishin Kula da Masallatan Harami Guda Biyu, Sheikh Abdulrahman Sudais ya ƙaddamar da sabuwar fasahar ganin dutsen Hajrul Aswad ta na’ura a masallacin Harami na Makka.

  Rahotanni sun baiyana cewa fasahar na cikin fasahohin zamani da za a yi baje-kolin su a masallatan Harami Guda biyu (na Makka da na Madina).

  Sai dai kuma Babban Ofishin ya ce hakan ba ya na nufin za a maye gurbin ainihin dutsen Hajrul Aswad ɗin ba.

  “Mu na da guraren tarihi na addini da na al’adu da doke ne mu mai da su na zamani ta amfani da fasahohin zamani ta yadda za mu gana da kowa ta hanyar fasahar zamani,” in ji Sudais.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here