Ƙungiyar Kamfanonin jigilar Hajji da Ummara, AHUON, ɓangaren shiyyar Jihar Kano, sun koka cewa sun yi asarar kusan naira biliyan 2 sakamakon dakatar da jirage da ga Nijeriya zuwa ƙasar Saudi Arebiya sakamakon ɓullar sabon nau’in korona mai suna Omicron.
A wata sanarwar bayan taron da su ka yi a ranar 10 ga watan Disamba, wacce su ka rabawa manema labarai a Kano a jiya Laraba, kamfanonin sun koka da cewa akwai bizar Ummara 1,600, ko wacce da tikitin jirgi da a ka kammala su kafin dakatarwar kuma ba za a iya amfani da su ba a halin yanzu.
A sanarwar, kamfanonin sun koka da cewa waɗan nan bizozin, wanda kowacce mafi ƙarancin farashin ta shine dubu ɗari 850 ce, kuma yanzu haka akwai bizozin da ba a ma kai ga kammala su ba.
Sun kuma yi ƙorafin cewa matakin da Saudiya ta ɗauka ya matuƙar girgiza su saboda ba a samu wani cikakken mai nau’in Omicron ɗan Nijeriya a Saudiya ba.
Masu kamfanunuwan sun kuma koka ga matakin da Hukumar Hajji ta Ƙasa NAHCON ta ɗauka na cewa dakatarwar ba ta shafi ma su Ummara ba.
Sun kuma yi kira ga gwamnatin taraiya da ta samu ta tattauna da ƙasar Saudiya domin ɗage dakatarwar, inda su kankara da cewa ƴan Nijeriya sun bi ƙa’idojin kariya da ga korona.