Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Ummaru Fintiri a jiya Laraba ya rantsar da sabon Shugaban Hukumar Alhazai Musulmai ta jihar, Imam Bappare Umar Kem.
Wannan ya zo ne bayan murabus ɗin da Sheikh Abubakar Ibrahim Daware ya yi a matsayin Shugaban Hukumar.
Da ya ke jawabi a gurin rantsarwar a gidan gwamnati, Fintiri ya taya sabon shugaban murna, inda ya umarce shi da ya yi riƙo da rantsuwa e da ya yi a yayin aikin sa.
Ya kuma hori sabon shugaban da ya yi amfani da ɗumbin ƙwarewar da ya ke da ita wajen bunƙasa harkar alhazai a jihar.
A nashi ɓangaren, Bappare Umar ya godewa Fintiri a bisa shugabancin da ya bashi.
Ya tabbatar da cewa zai ninka ƙoƙarin sa a matsayin sa na wanda ya shafe shekaru a Hukumar ya kuma kawo sauye-sauye na ci gaba a hukumar.
Ya kuma roƙi gwamnan da ya kawo ɗauki wajen gyaran hukumar, musamman ma wajen gyaran filin ta.