Saudiya ta hukunta kamfanonin hidimar alhazai

0
496

Ma’aikatar Hajji da Ummara ta Saudi Arebiya ta hukunta wasu kamfanunuwa na ƙasar masu yiwa alhazai hidima wadanda ta baiwa lasisi a Hajjin da ya gabata.

Maikatar ta ce an hukunta kamfanonin ne sakamakon gaza yiwa alhazai hidimar da ya kamata.

Da ga cikin hukuncin, ma’aikatar ta ƙwace lasisin da ta basu sannan kuma ta ci tarar su.

Kwamitin da Maikatar ta kafa domin bincikar masu ƙin yin hidima ta ƙwarai ga alhazan cikin gida shine ya ɗauki matakin hukuncin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here