Omicron: IHR ta yi kira ga Saudiya da ta janye dakatarwar tashin jirage a kan Nijeriya

0
337

Ƙungiya mai zaman kanta da ke Kawo Rahotanni kan Hajji da Ummara, mai suna Independent Hajj Reporters, IHR ta yi kira ga ƙasar Saudi Arebiya da ta janye takunkumin tashin jirage da ta ƙaƙabawa Nijeriya.

IHR ta kuma yi kira ga Gwamnatin Nijeriya da ta sanar da hanyoyi na harkar ƙwancen ƙasa da ƙasa da Saudiya domin ta ɗage takunkumin shigar jirage ƙasar da ga Nijeriya.

A sanarwar da Ibrahim Muhammad , Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa ya zantawa hannu a yau Juma’a, IHR ta yabawa Saudiya a bisa hoɓɓasar da ta ke yi na kare guraren ibada masu tsarki da lafiyar al’umma da ga kamuwa da sabon nau’in korona na Omicron.

Amma kuma, in ji ƙungiyar, “mu na fata dai Saudiya ta na da masaniyar cewa sauran kasashe irin su Amurka, Tarayyar Birtaniya, Canada, waɗanda da farko su ka sanya takunkumi a kan Nijeriya, yanzu sun ɗage wannan dakatarwar.

“Daɗin-daɗawa, Amurka ta ɗage dakatarwar a kan kasashe irin su Zimbabwe, Namibia, Lesotho, Eswatini, Mozambique da Malawai a kan Omicron, bayan da cibiyar Kula da yaɗuwar cututtuka Ta ƙasar ta amince da a dage takunkumin, saboda wannan dakatarwar ba dole ba ce wajen kare al’umma.

Sanarwar ta yi kira ga Saudiya da ta yi duba a kan shawarwarin da Hukumar Lafiya ta bayar na ɗage takunkumin tafiye-tafiye, inda ta yi kira ga ƙasar da ta cire dakatarwar a kan Nijeriya.

IHR ta ƙara da cewa matakin da Saudiya ta ɗauka na dakatar da jirage da ga Nijeriya ya sanya kamfanonin jigilar aljazai sun yi asarar kuɗaɗe da dama da su ka haura naira biliyan 1.

Ta koka da cewa kamfanonin sun durƙushe sabo da basussuka kuma babu wani tallafi a ƙasa da zai farfaɗo da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here