Korona: Dakatar da zuwa Ummara ya yi tsauri, in ji ɗan majalisa a Malaysia

0
533

Wani ɗan majalisa a Malaysia, mai wakiltar Shah Alam, Khalid Samad ya baiyana cewa hana tashin jirage zuwa Saudi Arebiya domin yin Ummara mataki ne da ya yi tsauri.

A cewa sa, a kwai matakai da Saudiya ya kamata ta ɗauka domin daƙile yaɗuwar korona tsakanin alhazan Ummara, kamar tsananta matakan kariya da ga kamuwa da cutar, ba wai a ɗauki matakin gaggawa na hana zuwa ibada ba.

Malaysia ta shiga ƙasashen da Saudiya ta dakatar da ga shiga ƙasar ta, inda matakin zai fara da ga 8 ga watan Janairu.

Ɗan majalisar ya yi kira ga Saudiya da ta yi duba a kan matakin ta samar da wani mai sauƙi, in da ya ce masu kamfanunuwan jigilar Hajji da Ummara a ƙasar sun kai masa ƙorafe-ƙorafe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here