An yi kira ga malamai da su tsananta addu’a kan kawo ƙarshen korona

0
92

Shugaban Hukumar Alhazai Musulmai ta Jihar Bauchi, Imam Abdulrahman Idris ya yi kira ga malan addinin Musulunci da su tsananta addu’a kan Allah Ya kawo ƙarshen annobar korona, musamman sabon nau’in Omicron.

A wata sanarwar da kakakin hukumar, Muhammad Sani Yunusa ya fitar, Shugaban yayi kiran ne a yayin wata ganawa da Malaman Musulunci a kan Hajjin bana.

Idris ya ce “ya kamata mu yi ta addu’a ba ƙaƙƙautawa domin Allah Ya kawo mana ƙarshen wannan annoba.”

Imam Idris ya ƙara da cewa addu’a ce kaɗai maganin wannan annoba, I’m da ya ce dole sai kowa ya bada gudunmawa sannan za a shawo kan lamarin.

Ya kuma roki malaman da su sayarwa da maniyyata kai wajen yin riƙo da matakan kariya da ga kamuwa da ga cutar korona, inda ya nuna cewa gwamnatin Saudiya ba za ta yarda da karya dokoki ba.

Ya kuma nuna cewa a kwanan nan Saudiya ta hana shigar jirage ƙasar da ga Nijeriya, inda ya ci alwashin haɗa gwiwa da masu jigilar Alhazai wajen yaƙar jita-jita.

A nasu jawaban, malaman sun yi kira ga al’umma da su gyara halayen su, su bi Ubangiji sannan su yi addu’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here