Saudiya za ta ƙara yawan masu zuwa Ummara da ga ƙasashen waje

0
108

A na sa ran ganin ƙaruwar zuwan alhazan Ummara da ga ƙasashen waje nan da watanni uku, har zuwa ƙarshen watan Ramadan, wanda shine lokacin da a ka fi samun yawan masu Ummara.

Wani mamba na Kwamitin kula da Harkokin Hajji, Ummara da Ziyara na Ƙasa, Saeed Bahashwan, ya baiyana cewa ɓangaren kula da Ummara na tsammanin ƙaruwar masu zuwa Ummara da ga ƙasashen waje a watanni ukun Rajab, Sha’aban da Ramadan.

Bahashwan ya danganta wannan ci gaban da irin cikakkun shirye-shiryen da ƙasashen wajen ke yi na jigilar alhazan su zuwa Saudiya.

A cewar sa, waɗannan ƙasashen sun haɗa da Indonesia, Pakistan, India, Egypt, Tunisia, Algeria, Uzbekistan da kuma Libya.

Bahashwan ya ƙara da cewa akwai adadin kamfanunuwa 201 da a ka baiwa lasisin yin aikin Ummara, in da ya ce a shirye su ke su yi hidima gangariyan ga alhazan da a ke tsammanin zuwan su, tun da ga saukar su da kuma komawar su ƙasashen su.

Ya kuma tabbatar da cewa kamfanunuwan a shirye su ke za su yi wa alhazan hidima da saukakawa alhazan yin ibadar.

Ya ce ƙasar Saudiyya ta samar da na’urori da za su taimakawa alhazan yin ibada cikin sauki a Masallatan Harami Guda Biyu na Makkah da Madina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here