Omicron: Ba za mu dakatar da yin Ummara ba duk da dawowar korona

0
402

Ma’aikatar Hajji da Ummara a Saudi Arebiya ta musanta jita-jitar da a ke na cewa za a dakatar da aikin Ummara sakamakon ƙaruwar annobar korona, bayan zuwan sabon nau’in cutar mai suna Omicron.

Wata majiya a ma’aikatar ta shaidawa jaridar Haramain Sharifain cewa Maikatar ba ta da niyyar dakatar da ummar, amma dai ta na kira ga baƙi da alhazan Ummara da su kiyaye da matakan kariya da mahukunta su ka ɓullo da su.

A kwanannan me dai Babban Ofishin Kula da Masallatan Harami Guda Biyu ya dawo da tsarin bada tazara da juna da kuma sanya takunkumin fuska a Masallatan biyu masu tsarki bayan ƙaruwar cutar ta koron.

“Mu na kira ga duk wani alhaji da masu ziyara da su kiyaye da matakan kariya na bada tazara da juna da sanya takunkumin fuska. Hakan zai tabbatar mana da kariyar kan mu da ta yan’uwa,” in ji Limamin Masallacin Harami na Makka, Sheikh Yasir Al Dossary a sallar Azahar ta yau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here