Omicron: Nigeria ta nemi Saudiya ta ɗage mata takunkumin zuwa ƙasar

0
933

Gwamnatin Nijeriya ta miƙawa Saudi Arebiya bukatarta ta ɗage dakatarwar shiga ƙasar da ta yi sakamakon ɓullar sabon nau’in korona na Omicron.

Ƙaramin Ministan Harkokin Waje, Ambasada Zubairu Dada ne ya miƙa buƙatar ga Ambasadan Saudiya a Nijeriya, Faisal bin Ebraheem Al-Ghamdi a jiya Alhamis a Abuja.

A ganawar, Dada ya nemi Saudiya da ta gaggauta ɗage dakatarwar da ta yi wa Nijeriya da ga shiga ƙasar sakamakon ɓullar Omicron.

“Tuni kasashen da su ka dakatar da Nijeriya su ka ɗage takunkumin nasu. Tuni su ka ɗage bayan da su ka lura da irin nasarorin da Nijeriya ta samu 2qjen yaƙar Omicron, da ma korona baki ɗaya.

Dada ya nuna cewa duk da cewa matakin da Saudiya ta ɗauka ta yi ne domin amfanin ƴan ƙasar ta, ya ce kamata ta yi duba da irin hoɓɓasar da Nijeriya ta yi kan yaƙi da korona, wanda shi ne ya sanya sauran ƙasashe su ka janye nasu takunkumin.

A nasa jawabin, Ambasadan Saudiya ɗin ya yabawa da nuna gamsuwa ga Nijeriya a bisa hoɓɓasar da ta yi na yaƙar Omicron.

Ya kuma yi alƙawarin miƙa buƙatar ta Nijeriya zuwa ga Masarautar Saudiyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here