Bayan tsaikon shekaru 2, za a dawo da buɗe-baki na haɗaka a Masallacin Annabi

0
656

Hukumar da ke Kula da Harkokin Masallacin Annabi a Madina, a ranar Alhamis ta sanar da cewa shirye-shirye sun yi nisa domin dawo da buɗe-baki na haɗaka a Masallacin Annabi idan watan Ramadan na bana ya zo.

Tun a ranar 24 ga watan Afrilu, 2020 a ka dakatar da buɗe-baki na haɗaka a Masallacin Annabi, a wani mataki na kariya, sakamakon annibar korona.

Hukumar ta ce za a shirya buɗe-baki na haɗakar a ƙarƙashin tsauraran matakai na kariya daga yaɗuwar korona.

Hukumar ta ƙara da cewa sai waɗanda a ka baiwa lasisi je za a bari su kai daguwar ledar da a ke shimfidawa a dora abinci a kai, wacce a ke kira da Sofra.

Ta ƙara da cewa sai guraren da a ka yarje ne za a shimfiɗa Sofra ɗin.

Hukumar ta ce nan gaba kaɗan za a sanar da adadin mutanen da a ke so su zauna a kan ko wacce Sofra.

Ta kuma ƙara da cewa dole sai dai masu kawo abincin sun baiwa kamfanunuwan dafa abinci su yi musu, inda ta ƙara da cewa dole su sanya mutane 5 a kan Sofra ɗaya idan a kwai tsarin bada tazara.

Idan kuma babu tsarin bada tazara, in ji Hukumar, to mutane 12 kawai za su bari su zauna a kan kowacce Sofra.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here