Kamfanin jirgin saman Indonesiya, Garuda ya shirya jigilar alhazai a Hajjin 2022

0
377

Kamfanin Jirgin Saman Ƙasar Indonesiya, Garuda Indonesia ya ce zai fara shirye-shiryen jigilar alhazai a Hajjin bana a yayin da zai rika kula da dokokin Saudi Arebiya, kamar yadda mahukuntan kamfanin su ka baiyana.

Shugaban kamfanin, Irfan Setiaputra ya kuma baiyana cewa, kamfanin sufurin jirgin saman zai yi wa fasinjojin sa hidima ingantacciya gami da kula da sharuɗɗan kariya da ga kamuwa da ga korona a yayin da su ke tashi zuwa ƙasa mai tsarki.

Ya ƙara da cewa tun tuni a ka samar da adadin jiragen da za su yi jigilar alhazan idan lokacin Hajjin ya yi.

Ya ce tuni kamfanin ya shirya da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da shiri da kuma nutsuwa ga alhazan Indonesiya da su ka hau jirgin.

Shugaban ya kuma ce kamfanin zai samar da manyan jirage da su ka haɗa da Boeing 777-300 da Airbus 330-300 domin alhazan.

Ya ce za su yi kokari su samar da adadin jiragen da za su yi daidai da adadin alhazan da Saudiya za ta baiwa Indonesiyan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here