Shugaban Hukumar Alhazai ta Kano ya kaiwa Mangal ziyarar ta’aziyar mahaifiyarsa

0
396

Shugaban Hukumar Alhazai taa Jihar Kano, Alhaji Muhammad Abba Dambatta, ya kai ziyarar ta’aziyya ga Alhaji Dahiru Mangal, Shugaban Kamfanin Sufurin Jirgin Sama na Max Air, a kan rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Murja Mangal.

Dambatta ya kai ziyarar ne tare da rakiyar Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Katsina, Suleiman Kuki, da kuma Daraktan Hukumar Alhazai na birnin tarayya (FCT), Alh Nasir Danmallam a jiya Litinin a Katsina.

A yayin ta’aziyyar, gaba ɗayansu sun yi addu’ar Allah Ya jiƙan marigayiyar da rahama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here