Cibiyar Hajji: Kungiyar Alhazai ta Jihohi ta yabawa NAHCON

    0
    456

    Shugabannin Hukumomin Alhazai na Jihohi, ƙarƙashin ƙungiyarsu ta Muryar Shugabannin Hukumomin Alhazai na Jihohi, sun sha alwashin mara baya ga Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) wanjen aiki da dukkanin tsare-tsaren da ta samar da zummar inganta harkokin Hajjin a Nijeriya daidai da tsarin duniya.

    Shugaban ƙungiyar kuma Daraktan Hukumar Alhazai ta Birnin Tarayya (FCT), Malam Muhammad Nasiru Danmallam ne ya bayyana hakan yayin da ya jagoranci mambobin ƙungiyar a wata ziyarar aiki zuwa Hukumar Hajji ta Nijeriya (NAHCON).

    Danmallam ya jaddada cewa, ɗaukacin mambobin ƙungiyar ta su na goyon bayan dukkanin tsare-tsaren da NAHCON ta bijiro da su don bunƙasa sha’anin aikin Hajji a Nijeriya, ta yadda zai yi daidai da na sauran ƙasashen duniya.

    Shugaban ƙungiyar ya ce, da ma dai jihohi sun kasance masu bibiyar cigaban da aka samu da suka haɗa da assasa cibiyar horarwa kam sha’anin Hajji, samar da asibitin ma’aikata da sauransu.

    Daga nan, ya yi jinjina ta musamman ga Shugaban NAHCON da kwamishinoni haɗa da hukumar gudanarwa na hukumar bisa gagarumar nasarar da suka samu.

    Kazalika, ya ce a matsayinsu na masu ruwa da tsaki cikin ayyukan Hajji, tuni ƙungiyarsu ta soma fata da addu’ar samun zarafin sauke farali a wannan shekara ga maniyyatan Nijeriya, kamar dai yadda ya roƙi Shugaban NAHCON ya taimaka ya shirya wani babban taron haɗin gwiwa da ƙungiyarsu don cigaban harkokin Hajjin Nijeriya.

    Sa’ilin da yake karɓar tawagar a ofishinsa, Shugaban NAHCON, Alhaji Zikirullah Hassan ya yi godiya da irin goyon bayan da ƙungiyar ke bai wa NAHCON musmman ma a lokutan da maniyyatan Nijeriya ba su samu zuwa hajji ba na shekaru biyu a jere.

    Alhaji Zikirullah Hassan ya ce, yana fatan shirye-shiryen hajjin 2022 za su kankama nan ba da daɗewa ba. Yana mai cewa, tuni NAHCON ta kasance cikin shirin ko-ta-kwana don samun nasarar aiwatar da ayyukanta da zarar Gwamnatin Saudiyya ta bada dama.

    Haka nan, ya ce nan ba da daɗewa ba za a buɗe asibitin da hukumar ta assasa, sannan an yi nisa da ƙoƙarin cimma ƙa’idojin samar da Cibiyar Horarwa Game da Hajji.

    Zikirullah ya yi na’am da buƙatar da shugaban ƙungiyar ya nema ta shirya taron haɗin gwiwa inda ya umarce shi da ya haɗa kai da wasu sassan NAHCON don cimma wannan ƙudiri.

    Sanarwar da ta fito ta hannun jami’in hulɗa da jama’a na MPWB, Muhammad Lawal Aliyu, ta nuna abubuwan da suka gudana yayin ziyarar har da miƙa kyautar yabo ga sabon Sakataren NAHCON, Dr. Rabi’u Abdullahi Kontagora, tare da yi masa addu’ar kammala wa’adinsa cikin nasara.

    Mahalarta taron sun haɗa da Mataimakin Shugaban Ƙungiyar kuma Sakataren Hukumar Alhazan Jihar Nasarawa, Alhaji Idris Ahmed Almakura, Shugaba Kwamishinonin NAHCON da sauran manyan ma’aikatan hukumar.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here