Hajjin 2022: Wani mazaunin England ya fara tattaki zuwa Makka

  0
  339

  Wani haifaffen England, Adam Muhammed, wanda ya fara tattaki a watan Agustan 2021 zuwa aMakka, Saudi Arebiya domin yin aikin Hajji daga Ingila da kafarsa, ya isa yankin Silivri na arewa maso yammacin Turkiyya.

  Muhammad ya fara bulaguro ɗin ne, wacce ya yi wa laƙabi da “Tafiya mai aminci”, ya samu taimakon wasu direbobi a kan hanya, inda har ya samu wani kare da ke shawagi kuma tuni su ka zama abokai ya kuma zame masa ɗan rakiya a kasar Sabiya.

  Baturen dan asalin kasar Iraqi ya tashi daga Ingila a watan Agustan 2021 zuwa Makka da kafa, balaguron da ya fara da nufin “fito da dukkan munanan abubuwa.”

  Muhammad, wanda ke tare da mafaɗacin abokinsa ya ɗaura niyyar isa Saudiyya a lokacin aikin hajji inda ya wuce kasar Siriya sannan ya wuce kasar Jordan kwanaki 35 da wuce Turkiyya.

  Yayin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Anadolu (AA) game da tafiyar tasa zuwa kasa mai tsarki, Muhammed dan kasar Iraqi da ya kwashe shekaru 25 yana zaune a Ingila ya ce: “Na fara tafiya ne a ranar 1 ga watan Agustan bara. Ina fatan zan yi shi cikin lokaci don aikin hajji na gaba.

  “Ina fatan duk tafiyar a kafa ce. Akwai wata murya mai karfi a cikina tana cewa zan iya zuwa Makka ta hanyar tafiya daga gidana. Ba zan iya yin watsi da wannan muryar ba. Yana cikin cikina kamar dutsen mai aman wuta,” in ji shi.

  Mohammed ya kara da cewa ya shirya tafiyar tsawon wata biyu kuma wata kungiyar Birtaniya ce ta taimaka masa.

  Mohammed ba shi ne mutum na farko da ya fara tattaki zuwa Makka daga Ingila ba. Wani dan Burtaniya Farid Feyadi shi ma ya yi irin wannan tafiya daga Landan a shekarar 2020 don karyata ra’ayoyin da kafafen yada labarai na Yamma suka yi game da Musulunci.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here