EFCC ta cafke Shugaban kamfanin sufurin jiragen sama na Medview bisa zargin zamba

0
353

Hukumar Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa, EFCC ta ka da kuma tsare Manajan-Daraktan Kamfanin Sufurin Jiragen Sama na Medview, Muneer Bankole, bisa zargin karkatar da kuɗaɗen da Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta biya shi, ta kuma daɗa masa dala 900,000, domin jigilar maniyyata aikin Hajji a shekarar 2019.

Daily Trust ta rawaito cewa Bankole, wanda ya isa shalkwatar EFCC da ke Abuja da misalin karfe 11 na safiyar yau Litinin, jami’an hukumar sun yi masa tambayoyi nan take.

Wata majiya mai tushe da ke da masaniya kan lamarin, ta bayyana cewa EFCC ta gayyaci Bankole ne kan zargin cewa NAHCON ta baiwa Bankole kashi 50 na kuɗin gudanar da aikin Hajji, sannan kuma ta daɗa masa dala 900,000 don jigilar alhazai alhazai a 2019.

Ana zargin cewa Bankole ya karbi kudaden ne a matsayin kafin alkalamin kwantaragin amma ba a ga komai a ƙasa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here